Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Manman Dauda, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Talata.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 1:30 na safe. Ya ce ‘yan sandan sun samu labarin ne da misalin karfe 01:30 na safe cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Rano inda suka yi awon gaba da wani Alhaji Na’ayya Gangarbi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Dauda ya ce, nan take rundunar hadin gwiwa ta jami’an sintiri na sashen, JTF da kuma masu yaki da masu garkuwa da mutane suka garzaya wurin. Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa an kwashe mutane biyu da suka samu raunukan harbin bindiga - Maskuru Ukaisha a kafarsa ta dama da Salisu Ibrahim a kafadarsa ta hagu, inda aka garzaya da su babban asibitin Rogo domin samun kulawa.
A cewarsa, an tura karin jami’an tsaro dauke da makamai zuwa yankin domin bibiyar ’yan bindigar da duk wasu bata-gari da ke kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin mazauna yankin.
“An tura jami’an tsaro dauke da makamai da sauran tawagogin dabara tare da ‘yan banga zuwa yankin domin samun nasarar ceto wadanda lamarin ya shafa,” inji shi.
Ya ce an fara gudanar da bincike domin kamo wadanda suka sace tare da kubutar da wadanda abin ya shafa. (NAN)