Wannan ita ce kwallo ta 702 da dan wasan, dan kasar Argentina ya ci a nahiyar Turai kuma a yanzu shi ne kan gaba wajen zura kwallo a raga a kungiyoyin kwallon kafa na Turai, inda ya haura na abokin hamayyarsa, Cristiano Ronaldo da ya ci 701.
Dan wasan na PSG ya samu nasarar buga wasanni 105 kasa da kyaftin din Al-Nassr, Ronaldo.
Kwallon da Messi ya ci a minti na 26 ita ce ta 14 da ya ci a gasar Ligue 1 ta bana, inda ya kuma ya taimaka aka zura kwallaye 13.
Ya kasance kai tsaye ya ba gudunmawa fiye da kowa ya zuwa yanzu a gasar.
Yayin da ya ke taka leda a Barcelona, dan wasan mai shekaru 35 ya ci kwallaye 672 a wasanni 778.
Bayan buga wasanni 68 ciki har da wasan Nice, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai a yanzu ya ci wa PSG kwallaye 30.