Jam'iyyar mu ta APC jam'iyya ce mai mulki kuma tayi duk mai yiwuwa don ganin farantawa al'umma amma haƙan ta bai cimma ruwa ba, ba don komai ba sai don son kai na wasu tsiraran cikin jam'iyyar, saboda haka ta batawa mutane sosai, shi yasa duk inda aka ce taci zabe sai an kai ruwa rana kafin ayi nasara don ko a jihar zababben shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinibu babu wato Lagos sai da aka ɗaga zaben wasu akwatunan da dama sannan daga baya akai ruwa akai tsaki aka samu aka ƙwaci gwamnatin da ƙyar da siddin goshi. Muma a Kano an samu irin wannan to amma ba kamar can ba domin mu a nan manyan shuwagabannin jam'iyyar sun rigada sun kashe jam'iyyar shi yasa da aka zo zaben aka bada rata mai yawan gaske duk anyi iya ƙoƙarin ganin an kawo ta amma nagaba yayi gaba na baya sai labari...
Duk wanda zai yi zabe a kano ya zabi raayinsa domin mu masu laifi ne shi yasa al'umma suka zabi iya waÉ—anda sukai musu aiki musamman mutanen kano ta Arewa.