''Rashin iya siyasa ne da rashin sanin doka yasa suke É—aukar hoton mahaifiya ta suna zagi a kafafan sada zumunta, zuwa yanzu mun samu mutum 35''
Al'ummar Jihar Kano sun bani mamaki duba da yadda suke gudanar da siyasa musamman magoya bayan ɗariƙar kwankwasiyya domin duk inda ake neman adawa irin ta siyasa idan aka same su anzo ƙarshe, babu wanda suke kuma ƙin jinin ayi musu adawa irin su domin basa iya jurewa, Nayi waƙa a shekarar 2011 mai taken Tabare! sunfi kowa murna da ita domin an soki babban wanda sukewa adawa a kano Mal. Ibrahim Shekarau haka da aka karbi mulki bayan da GANDUJE ya karbi kano shekarar 2019 shima akai masa waƙa amma bata musu daɗi ba saboda yayi nasara a kotu''. Abin lura a nan shine : babu wanda a cikin su yake da hujja wadda zai ce an kama sunan jagoran sa a siyasa an zaga sai dai yace yana zargi, sunfi kowa sanin haka amma duk da haka suke ɗaukar hoton mahaifiya ta suke zagi, na shirya tsaf domin maka duk wanda ya zagi mahaifiya ta a kotu.