Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa, NAFDAC ta rufe wasu shaguna guda biyu a Abuja bisa zargin sayar da magunguna da ba ingantattu ba.
Shagunan na nan a Zuba Central motor park kuma babbar kasuwar Utako, inda aka rufe su jiya Laraba.
Magungunan da aka kama a shagunan sun hada da Hajiya Ayesha Snuff, AK47, Bulletproof da kuma Hajiya Aysha Maisanda”.
Mataimakin Daraktan Bincike da Tursasawa na hukumar, Tamanuwa Baba, ya ce an bankado shagunan ne bayan sun samu bayanan sirri.
Ya ce "magungunan na ƙarfin maza ne kuma wasu daga cikin su ma a Ghana a ke yin su.
"A dakin gwaje-gwaje na NAFDAC mu ka gano cewa magungunan ba ingantattu ba ne kuma su ma dauke da wani sinadari mai suna Pyridine wanda ya ke da illa ga jikin dan Adam," in ji shi.
Bana ya ce tuni su ka kama mai dillancon magungunan har sai asalin masu shagunan sun mika kansu Ga hukumar.