Kofa, wanda ya zama zaɓaɓɓen dan majalisar wakilai ta tarayya, ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Channels TV a jiya Laraba.
Ya ce “tun da dadewa ina da alaka mai karfi da jagoran NNPP na Æ™asa Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda shi ne ya koya min siyasa.
“A daya bangaren kuma, ba a son zaman mu a APC. Gwamnan baya son da yawar mu a jam’iyyar, shi ya sa ya riÆ™a yin yadda zai yi ya kore mu da ga jam’iyyar.
“Shi (Ganduje) yana fada da mu, ya tabbatar ba mu samu komai ba, ba mu iya numfashi a APC ba.
“sai mu ka fice mu ka tattara kan mu mu ka fice, sannan mu ka koya masa darasin siyasar da ba zai taba mantawa ba a rayuwarsa.
“Kuma a karshen wannan rana, ya haifar wa da APC asarar ‘yan majalisar wakilai 18, ciki har da wakilai kusan shida ko bakwai da jiga-jigai ne.
“Ya yi wa APC asarar Æ´an majalisar jiha 34 kuma ina mai tabbatar maka da cewa dukkan su masu nagarta ne,” in ji Kofa