Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da kafafen yada labarai suka yada cewa ya amince da Dino Melaye a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar, gabanin zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
A wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai magana da yawun sa, Paul Ibe a yau Talata, Mista Abubakar ya musanta cewa ya nada dan takara a jam’iyyar ta PDP.
Ya ce, a matsayinsa na cikakken dan siyasa, alamar gwagwarmayar siyasarsa ita ce samar da dimokuradiyya ta cikin gida a siyasar jam’iyya.
"'Kamar yadda kafafen yada labarai da dama suka ruwaito, wasu dattawan jam’iyyar PDP reshen jihar Kogi, karkashin jagorancin wani Ibrahim Dansofo sun bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar da ya gaggauta janye amincewar da ake zarginsa da shi tare da barin jerin sunayen wakilai na asali daga kananan hukumomi 21 na jihar.
Da ya ke mayar da martani, Mista Ibe ya ce, “An jawo hankalin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, a wasu rahotannin kafafen yada labarai da ke nuna cewa ya sa baki har ya nuna wanda ya ke yi a ƴan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi mai zuwa.
“Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa irin wadannan rahotannin kafafen yada labarai na karya ne kuma kage ne.
"Gogewar Atiku da kuma riƙo da dimokuraɗiyya ya wuce ya yi nune a ƴan takara," in ji I've.