Kotun Majistire da ke gidan Murtala a Kano ta umarci wani mutum, Isyaku Shu’aibu da ke unguwar Ja’en da ya yanka zakaransa.
Freedom Radio ta rawaito cewa maƙwabcin mutumin, Malam Yusuf Muhammad, shima mazaunin unguwar ta Ja’en ne ya shigar da ƙara a kotun bisa cewa zakaran na shiga haƙƙinsa ta hanyar hana shi barci da yawan cara.
Amma ko da aka karanto wa wanda ake ƙara tuhumar, ya ce, gaskiya ne zakaran na yawan yin cara kuma zai yanka shi ne a bikin “Good Friday” , don haka ya roƙi kotun da ta sahale masa zuwa ranar.
Freedom Radio ta rawaito mai shari’a Halima Wali ta amince inda ta umarci ya killace Zakaran kuma ya yanka shi a Jumu’a mai zuwa wato ranar “Good Friday” ɗin.