Magoya bayan jam’iyyar PDP a Jihar Rivers, sun gudanar da zanga-zanga a garin Fatakwal tare da boka don nuna kin goyon bayansu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Masu zanga-zangar na dauke da kayan tsibbu, wanda wannan ita ranar su ta biyu da suke rajin INEC ta ba su damar duba kayayyakin zaben da aka yi amfani da su a jihar.
A jiya Litinin sun kai wa dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar, Tonye Cole hari a yayin da suka yi arangama a hanyarsu ta zuwa ofishin INEC.
A yau Talata bayan dawowarsu bakin zanga-zangar an hangi shugaban karamar hukumar Ikwerre, Samuel Nwanosike sanye da farin kaya da hula dauke da wasu kayan tsafi, yana furta wasu kalamai.