Wani direba da ya doke ƙarfen hana shigewar manyan motoci a kan gasar Ado Bayero, wacce a ka fi sani da gadar Lado a daren jiya Lahadi a jihar Kano, ya bayyana dalilin da ya sanya hau kan gadar.
A safiyar yau Litinin ne dai aka wayi gari a ka ga wata babbar mota ta yi awon-gaba da ƙarfen da aka saka a bakin gadar Lado don hana manyan motoci hawa, inda ta raba ƙarfen biyu, ita kuma ta lollotse.
Sai dai kuma a tattaunawar da Freedom Radio ta yi da direban, ya ce birki ne ya shanye masa, inda ya ga gwara ya hau kan gadar domin gujewa afkuwar hadari mafi muni.
A cewar sa, da ya taho sai birkin motar ya shanye kuma sai ya ga cewa idan ya ce zai bi ta ƙasa, to lallai zai hau kan motoci da yawa kuma hakan ka iya haifar da rashin rayuka da jikkata sosai.
"Shi ne kawai na haye saman gadar na kuma doke karfen nan. Amma ni ban ji ciwo ba alhamdulillah. Da na ce zan bi ta Æ™asa, to fa da na take mutane da yawa sabo da birkin ne ya shanye,” in ji shi.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa lamarin ya haifar da cecekuce a kafafen sadarwa, inda wasu ke kira da a hukunta direban domin ya zama darasi ga wasu masu kunne kashi.