Umar Abdu Umar, Dan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya tsaya takarar majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC, ya maka Tijjani Abdulkadir Jobe na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ce ta bayyana Jobe a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a mazabar Rimin-Gado, Dawakin-Tofa da Tofa.
Umar, ta bakin lauyansa, Barista A.T Falola, ya kuma kalubalanci INEC kan ayyana Jobe a matsayin dan takarar da ya samu rinjayen kuri’un da aka kada a lokacin zaben.
Da ya ke gabatar da kara a gaban kotun, Falola ya roki kotun da ta gudanar da shari'ar a kan Jobe da kuma jam'iyar NNPP mai sakatariya a Sharadi, Kano