Jami’an tsaro da ke aiki a harabar majalisar tarayya da ke Abuja sun cafke wasu hadiman ‘yan majalisa da ma’aikatan majalisar da laifin tafka sata da kwashe wasu kayayyaki masu daraja a ofisoshin Æ´an majalisa.
Wasu daga cikin kayayyakin sun hada da na'urorin talabijin, kantocin ajiye littattafai, na'urorin lantarki, kwamfutoci, firintoci, kayan daki, na'urorin sanyaya daki, kafet, da na'urorin wutar lantarki na doka.
Sunday PUNCH ta tattaro cewa ‘yan majalisar dattawa da ta wakilai masu barin gado da wadanda suka sake cin zaÉ“e na Æ™oÆ™arin fitar da tsofaffin kayayyakin ofisoshin su don saka sabbin kamar yadda ya ke a al'ada.
Sai dai jami’an tsaro da harabar majalisar dokokin kasar sun cafke wasu daga cikin mataimakan ‘yan majalisar bisa yunkurin fitar da wasu kayayyaki ba tare da izini ba.
A cewar majiyoyi da dama, an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da su ke kokarin ficewa daga cikin harabar ba tare da takardar izinin fita da kayayyakin ba.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sajan mai kula da Majalisar, Chuks Obaloje, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai iya bayar da cikakken bayani ba.
“Eh, an kama wasu mutane ne a yayin da suke kokarin fita da wasu kayayyaki daga Majalisar Dokoki ta kasa. Amma ban kasance kan aiki a ranar da abin ya faru ba, don haka ba zan iya ba ku cikakken bayani ba. Sai dai a tuntubi Sashen Laifuffuka na Majalisar Tarayya,” Obaloje ya shaida wa wakilin SUNDAY PUNCH a lokacin da aka tuntube shi a ranar Juma’a.
Jami’in ‘yan sanda mai kula da harabar majalisar dokokin kasar, Alex Annagu ya ki cewa komai kan lamarin.
