Shugaban kwamitin tsaftace Kano, Ambasada Ahmadu Haruna Zago, ya bayyana cewa sun cimma kusan kaso 80% na aikin kwashe shara da aka jigbe akan wasu titunan birnin Kano,
kuma da sannu za su cimma dukkan nasarar da ake bukata, wajen ganin an tsaftace Kano daga Ƙazanta.
Ahmadu Zago ya bayyana haka ne yayin rangadin duba aikin kwashe sharar, harma wasu mazauna Unguwar Ƙofar Ruwa su ka bayyana jin dadinsu akan wannan aiki da ake gudanarwa a halin yanzu.
Cikin jawabinsa, Zago ya godewa al'ummar jihar Kano, tare da kira a gare su, da su cigaba da basu hadin kai da goyon baya domin ganin anyi dukkan abinda ya dace.
Tuni dai sabuwar gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, ta daura damarar yaƙi da ƙazanta a fadin jihar, harma da ƙaddamar da shirin tsaftace Kano, tare da samo gudummawar motocin dibar shara, domin gwamnatin ta ce tsohuwar gwamnatin Ganduje ba ta bar mata motocin kwasar shara ba sai guda biyu kacal.