Yadda aka hadu a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake babban Birnin tarayya Abuja, tsakanin Sanata Ibrahim Shekarau da amininsa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Anjima raban da a hangi aminan su biyu tun lokacin da suka hade a inuwa guda
Inda Malam Ibrahim shekarau yakoma jami'iyyar Engr Rabi'u Musa Kwankwaso bayan zawarcinsa da Kwankwaso yayi hargidan Shekarau din
Sai dai kuma tafiyar bata cimma yadda sukesoba akai hannun riga tsakannin gwarazan siyasar biyu na jihar kano
Sai gashi a yammacin wannan rana hanya ta hadasu kuma har angesu suna hira da far'a a fuskar kowannansu
Sai dai satin daya gabata anjiyo Sanata Ibrahim shekarau yayin tattaunawa da wata kafa yana bayyana cewar shida Sanata Rabi'u Kwankwaso aminan juna ne