Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce ta gano wani ɗakin gwaji da ake haɗa miyagun ƙwayoyi a asirce.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Asabar ta ce jami'an hukumar ne suka gano ɗakin gwajin wanda ake sarrafa miyagun ƙwayoyin a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Sanarwar ta ce an samu wasu ƙwayoyi da aka sarrafa a ɗakin a lokacin da jami'an hukumar suka kai samamen.
Hukumar ta ce ta samu nasarar ƙaddamar da samamen ne bayan da ta samu bayanan sirri game cewa ana sarrafa miyagun ƙwayoyi a wurin.
Haka kuma NDLEA ta ce tana ƙoƙari wajen ganin ta kama mutumin da ya mallaki wurin.