Wannan rana ce da tarihin kasar ba zai manta da ita ba saboda a ranar ne aka gudanar da zaben Najeriya na 1993, ko da yake har kawo yanzu hukumar zaben Najeriyar ba ta sanar da wanda ya ci shi ba.
To sai dai kuma alamu sun nuna cewa dan takarar jam'iyyar SDP, wato Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ne ya lashe zaben inda ya kayar da abokin takararsa na jam'iyyar NRC Bashir Othman Tofa.
An dai ki sanar da sakamakon zaben ne saboda soke zaben da gwamnatin mulkin soja a karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi.Soke zaben dai ya janyo gagarumar tirjiya daga 'yan jam'iyyar SDP da kuma 'yan gwagwarmaya da ke da rajin kafa gwamnatin farar hula a wancan lokaci abin da ya kai ga tsare wasunsu da dama ciki har da Abiola.
Wasu ‘yan kasar dai sun bayyana ranar a matsayin ranar da ta fara tabbatar da mulkin dimokaradiya a Æ™asar.