Yayin wata tattaunawa da BBC, Umar Namadi ya ce kamar yadda tsohon gwamna ya yi aiki da su, shi ma ya yi aiki da su a a lokacin yana matsayin mataimakin gwamna kuma ya san irin rawar da suka taka a tsohuwar gwamnatin.
''Duka wadannan kwamishinoni da ake ganin na sake naɗawa da suka yi aiki ƙarƙashin tsohon gwamna, ni ma sun yi aiki ƙarƙashina a lokacin da nake riƙe da muƙamin mataimakin gwamna, saboda haka na san kowa, na san abin da zai yi, na kuma san abin da ba zai iya yi ba''.
Tun bayan bayyana sunayen sabbin kwamishinonin jihar ne, wasu suka riƙa sukar gwamnatin da cewa tsoffin jami'an gwamnatin da ta gabata ne suka mamaye sunayen kwamishinonin, maimakon bayar da dama ga wasu sabbin fuskoki.
To sai dai Gwamna Namadi ya ce yana ganin babu laifi kan wannan mataki, ''abin da kawai muke buƙata shi ne waye zai iya riƙe amana, waye zai iya yi wa mutanen jihar jigawa abin da ya dace'', in ji Gwamna Namadi