Ana fargabar cewa mutane da dama sun mutu a babban Masallacin Zariya da ke ƙofar fada, bayan ruftawar ginin mai tsohon tarihi na Masarautar Zazzau.
Wata majiya daga fadar Sarkin Zazzau ta ce ana ci gaba da aikin ceto bayan aukuwar lamarin a Juma'ar nan.
Babu cikakken bayani a yanzu kan yadda lamarin ya faru.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna mutane ɗauke da shebura suna yashe ƙasar da ta rufta a tsakiyar masallacin.
An kuma ga wani da ke nuna yadda rufin ginin a wani sashe na tsakiyar masallacin ya ɓare har ana iya hango sama a lokacin da aikin ceton ke ci gaba da gudana.
Masallacin, tsohon gini ne da aka yi shi cikin fasali irin na gine-ginen Hausawa da yawan ginshiƙai da ke tashi daga jikin ganuwa har zuwa rufin ginin, sannan su tanƙwara su sauka a ɗaya ɓangaren.