Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta fara aiwatar da tsarin 'Ba aiki, ba albashi' ga mambobin ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasar da ke gudanar da yaji aikin sai-baba-ta-gani a fadin ƙasar.
Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da darakta kula da ayyukan asibitocin ƙasar Dakta Andrew Noah ya aike wa manyan daraktocin asibitocin gwamnatin tarayya, kamar yadda jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito.
WasiÆ™ar ta ce “Ina mai sanar da ku cewa ku riÆ™a É—aukar sunayen likitocin da suka zo aiki, tare da tuura sunayen zuwa ma'aikatar lafiya a kowanne wata''.
Ya kuma ce ma'aikatar lafiyar kasar tare da hukumar ƙwadago ta ƙasar da sakataren gwamnatin tarayya da majalisar dokoki ta ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki a gwamnati sun sha yin zama da ƙungiyar likitocin don jan hankalinsu cewa su jingine yajin aikin da take yi a fadin ƙasar.
A ranar 26 ga watan Yuli ne dai ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta sanar da tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani a fadin ƙasar samakon kasa biya musu buƙatunsu daga ɓangaren gwamnatin tarayya.