Masu fafutuka da lauyoyin kare 'yancin ɗan'adam a Najeriya na ci gaba da nuna damuwa a kan ci gaba da tsare dakataccen shugaban babbar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC).
Suna kafa hujja da cewa ci gaba da tsare Abdurrasheed Bawa tsawon lokaci, ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba, abu ne da ya saɓa wa tsarin mulki.
Tsawon kwana 67 kenan, Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS take tsare da dakataccen shugaban na EFCC.
Fitaccen lauyan nan mai kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya, Femi Falana, ya yi kira ga hukumar ta gaggauta sakin dakataccen shugaban na EFCC, ba tare da ɓata lokaci ba.
A cewarsa, umarnin tsare Abdurrasheed Bawa da wata kotun majistare ta bayar, ba ya kan ƙa'ida saboda babu wata kotun majistre da ke da ikon ba da umarnin tsare wanda ake zargi tsawon fiye da wata biyu, ba tare da an tuhume shi ba bisa tanadin tsarin mulki.
Babu wanda zai iya faɗar halin da dakataccen shugaban na EFCCn yake ciki tun bayan kama shi, a cewar shugaban gamayyar ƙungiyoyin fararen hula na arewacin Najeriya, Ambasada Ibrahim Wayya.
Ya ce duk ƙoƙari da suka yi, na ji daga Bawa, ya ci tura.
Ya ce suna ta ƙoƙarin tuntuɓar waɗanda ya dace su san halin da yake ciki.
"Har yanzu babu wata kafa da aka samu da za ta iya ba ka bayanai a kan halin da yake ciki.
Mun yi ƙoƙarin samun waɗanda ke da kusanci da shi, don jin ko akwai wani bayani, amma su kansu suna jin tsoron magana, wataƙila suna fuskantar barazana," in ji Wayya.
Ya ce duk fafutukar da suke yi ma a yanzu ita ce ta sanin me yake faruwa da shi.