Hakan na zuwa ne bayan matsayar da aka cimma a taron shugabannin jam'iyyar da aka yi.
Da ma tun kafin tabbatar wa tsohon gwamnan na Kano da muƙamin, an shafe kwankai da dama ana raɗe-raɗin cewar shugaban ƙasar Bola Tinubu ya zaɓe shi domin karɓar muƙamin.
Ganduje ya karɓi muƙamin ne a lokacin da ake ganin jam'iyyar na fuskantar manyan ƙalubale.
Har yanzu ana ci gaba da raɗe-raɗi game da dalilan da suka sanya tsohon shugaban jam'iyyar, Abdullahi Adamu ya ajiye muƙamin rana tsaka.
Amma bayanai masu ƙarfi sun tabbatar da cewa ya sauka ne sanadiyyar rashin jituwar da ke tsakaninsa da wasu jiga-jigan gwamnatin Shugaban Bola Ahmed Tinubu.
To amma waɗanne ƙalubale ne ake ganin za su fi girma a lokacin shugabancin Ganduje na jam'iyyar APC?
Rarrabuwar kan ƴaƴan jam'iyya
Rarrabuwar kan da ke a jam'iyyar ta APC na daga cikin abubuwan da ake ganin sun yi sanadin ajiye aikin Sanata Abdullahi Adamu.
Tun gabanin babban zaɓen ƙasar na 2023, kawunan ƴaƴan jam'iyyar sun rabu.
Ta kai ga cewa an zargi wasu ƴaƴan jam'iyyar da rashin goyon bayan Bola Ahmed Tinubu lokacin da yake takarar kujerar shugaban ƙasar.
Wannan ɓaraka ta fito ƙarara bayan da wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar suka garzaya kotu domin nuna adawa da wasu daga cikin manufofin tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari.
Sun yi zargin cewa an ɓullo da manufofin ne domin yin zagon ƙasa ga nasarar Bola Tinubu.
Wannan rarrabuwar kawuna ta kai har bayan zaɓen shugaban ƙasa.
A lokacin rabon muƙaman shugabancin Majalisar Dokokin Tarayya, an ambato tsohon shugaban jam'iyyar, Abdullahi Adamu na cewa an raba muƙaman ne ba tare da masaniyar shugabancin jam'iyya ba.
Haka nan akwai wasu ƴaƴan jam'iyyar ta APC da ke ganin bai kamata a ɗauke muƙamin shugaban jam'iyyar daga yankin arewa ta tsakiyar ƙasar ba, inda daga nan ne tsohon shugaban jam'iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya fito.
Saboda haka ne masana harkar siyasa kamar Farfesa Kamilu Fagge, malami a jami'ar Bayero da ke Kano, ke ganin cewa wannan na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da sabon shugaban na APC zai ci karo da su.
Kuma a cewar wasu masu sharhi, idan har Ganduje ya samu nasarar haɗa kan ƴab jam'iyyar mai mulkin Najeriya a daidai wannan lokaci, to tabbas za a iya cewa ya fara da ƙafar dama.