Wata sanarwa da dakarun taron ƙasar suka fitar, ta ce maharan sun isa garin Sanam a kan babura inda suka yi wa sojojin kwantan ɓauna.
Garin Sanam na a yankin Tillaberi da ke iyaka da ƙasashen Mali da Burkina Faso, wanda ya kasance yankin da ya fi fuskantar hare-hare.
Rahotanni sun bayyana cewa a ɓangaren masu iƙirarin jihadin, an kashe mutum goma.
A ranar 9 ga watan Agusta, aka kashe wasu sojojin Nijar biyar a wani hari a yankin na Tillaberi, a cewar sojojin da suka hamɓarar da shugaban ƙasar Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.