Ƴan majalisar sun gargaɗi Shugaban ƙasar, Nana Akufo-Addo cewa ya dakatar da shirin tura sojojin ƙasar domin zuwa Nijar.
"Majalisar dokokin Ghana ba ta tattauna ba kan lamarin kamar yadda sauran ƙasashe suka yi har ma da ɗaukan mataki, in ji Samuel Ablakwa, wani ɗan majalisa a kwamitin kula da harkokin ƙasashen waje.
Ya ce Shugaba Akufo-Addo ba sai ya ji ta baki ƴan ƙasar Ghana ba kan lamarin , saboda tura sojoji Nijar ba shi ne mafita ba.
Ƴan majalisar ƙasar ɓangaren marasa rinjaye sun ce abin da ya kamata a yi shi ne bin hanyar diflomasiyya da kuma tattauna.
"Ba abu mai kyau bane tura sojojin Ghana zuwa Nijar domin zub da jini, kuma muddin ba a yi hankali, abin zai sake jefa yankin cikin tashin hankali," in ji Mista Ablakwa.
Ƴan majalisar sun ce ya kamata a yi amfani da kuɗin da ake da shi wajen warware matsin tattalin arziki da ƙasar ke fusknta baya nciyo rancen $3b daga Asusun IMF maimakon tura sojoji zuwa faɗa.