Wasu da ake zargin ƴan bindiga, sun kai hari kamarar hukumar Bungudu na jihar Zamfara, inda suka kashe mutum ɗaya tare kuma da sace wasu guda bakwai.
Wani mazaunin garin, Ishaq Bungudu ya faɗa wa gidan talabijin na Channels cewa ƴan bindigar sun yi garin dirar mikiya ne da safiyar Litinin ɗin nan ɗauke da muggan makamai, inda suka yi ta harbi kan mai uwa-da-wabi har suka kashe mutum ɗaya nan take.
Ya ce an kuma yi awon gaba da wasu mutum bakawai, ciki har da ɗan Sarkin Bungudu Abdulrahman Hassan da wani tsohon jami'in asusun bunƙasa aikin gona a jihar (IFAD) Abubakar S/Fada.
Ishaq ya nuna damuwa kan ƙaruwar hare-hare a karamar hukumar ta Bungudu duk da cewa tana kusa da Gusau, babban birnin jihar.
Ya buƙaci gwamna Dauda Lawal da ya taimaka wajen naɗa masu taimaka masa ta ɓangaren tsaro.
"Ana far mana a kullu yaumin. Ba mu san wajen da za mu kai kukan mu ba, saboda gwamna bai naɗa masu taimaka masa ta ɓangaren tsaro ba tun hawansa mulki. Ya kamata ya yi naɗe-naɗen domin mu san wanda za mu kira idan an kawo mana hari," in ji shi.
Karamar hukumar Bungudu dai na da nisan kilomita 21 da Gusau babban birnin jihar.
Idan za a iya tunawa, a watan da ya gabata an kashe ƴan sanda huɗu a karamar hukumar a wasu hare-hare da ƴan bindigar suka kai.