Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang shi ya bayyana haka lokacin da ya karɓi bakuncin kwamitin majalisar wakilai da yake gudanar da bincike kan badakalar naira tiriliyan 2.3 na kuɗaɗen asusun tallafawa jami'o'i (TETFUND) a Jos a karshen mako.
Mutfwang ya faɗa wa kwamitin wanda ya samu jagorancin Unyime Idem cewa gwamnonin shiyyar za su yi magana da harshe ɗaya kan matsaloli da suke fuskanta, musamman rashin tsaro.
Duk da cewa gwamnan bai yi wani ƙarin haske ba kan irin shirin da suke yi, ya ce shi da takwarorinsa za su tashi tsaye don ganin an samar da ƴan sandan jihohi.
Ya yi kira ga majalisar wakilan Najeriya da su goyi bayan duk kudurori da aka kawo waɗanda suka danganci tsaro.
Jihohin arewa maso tsakiyar Najeriya sun kunshi Benue, Plateau, Nasarawa, Niger da Kwara, inda shiyyar ta kasance ɗaya daga cikin wadda ke fama da matsalar tsaro a ƙasar.
Rikicin manoma da makiyaya na cikin abubuwan da suke yi wa shiyyar babbar barazana.
Ko a farkon watan nan, an ruwaito kashe mutum 21 a wani hari da wasu suka kai kauyukan jihar Plateau.