Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya tabbatar da zaɓen Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar.
An zaɓi Ganduje ne a lokacin taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar na 12 da aka gudanar a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan ƙusoshin jam'iyyar da suka halarci taron kwamitin zartarwar APC na ranar Alhamis.
Ranar 17 ga watan Yuli ne tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da babban sakataren APC Sanata Iyiola Omisore suka sanar da ajiye muƙamansu.