Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin ƙungiyoyin masu haya da motoci a filin jirgin.
Hukumar ta shawarci fasinjoji da su yi amfani da duk wata hanyar sufuri amintacciya domin tabbatar da tsaron su a ciki da wajen filin jirgin.
"Za a dawo da sufurin da zaran kamfanonin sun daidaita kan su,"i n ji sanarwar ta FAAN, wadda ta samu sa hannun daraktan hulÉ—a da jama'a na hukumar, Abdullahi Yakubu-Funtua.