Matakin da ke zuwa mako ɗaya bayan da sojojin suka yi juyin mulki a Nijar, tare da bayyana aniyarsu ta raba gari da ƙasar Faransa.
Da misalin Karfe 3 na yammacin Yau ne aka lura da katse shirye shiryen gidan rediyon RFI da tashar Talabijin ta France 24.
Hakan ya sa mutane su ka fara tambayar abinda ke faruwa da kuma dalilan da suka sa majalisar ceton ta ƙasa daukar irin wannan mataki, ko da yake waɗannan tashoshi sun fuskanci irin wannan matsala a ƙasashen Mali da Burkina Faso.
Sai dai tun farkon wannan juyin milki an ji wasu ƙungiyoyi na farar hula suna kira ga hukumomin mulkin sojan da su kori kafofin yaɗa labarun na ƙetare.
Sakataren yaɗa labarai na cibiyar ƴan jarida ta ƙasa, Souleymane Brah, ya yi Allah wadai da matakin ya kuma yi kira da hukumomin su janye matakin.
A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar tashoshin na Rfi da France 24 sun nuna rashin jin daÉ—in su kan lamarin.