Sahaidu sun faɗa wa BBC Arabic cewa an ƙara jibge dakarun sojan Sudan a birnin Al-Fula na jihar ta Kordofan, suna masu cewa ƙazamar fafatawar da ɓangarorin suka yi ta lalata sassan birnin da yawa.
A Nyala, babban birnin jihar Darfur ta Kudu, shaidun sun ce faɗa ya ɗan lafa, amma ana ci gaba da jin ƙarar harbe-harbe.
Mazauna yankin sun ce arangamar da aka shafe kwana uku ana yi ta ɗaiɗaita yankin, yayin da ake ci gaba da kashe fararen hula.
A gefe guda kuma, jami'an sojan Sudan sun tabbatar da cewa sun yi ruwan wuta kan wasu sansanonin RSF a kudancin birnin Khartoum.
Wata majiya ta ce hare-haren sun fi ƙamari a unguwannin Jabra, da Abu Adam, da kuma Kalakia.