Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa tsohon Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru ministan tsaron ƙasar.
Kazalika, tsohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ne zai taimaka masa a matsayin ƙaramin ministan tsaro.
Tsohon Gwamnan jihar Ribas da ke kudancin ƙasar, Nyesom Wike, shi ne ministan Abuja, yayin da Maryam Mairiga daga Kano za ta yi aiki a matsayin ƙaramar ministar Abuja.
Wata sanarwa ce daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana sunayen ministocin da ma'aikatunsu a yammacin Laraba.
Mutum 45 cikin 47 majalisar dattawa ta tantance kuma ta tabbatar a matsayin ministocin na Tinubu, abin da ke nufin za a sanar da sauran nan gaba.
Ga jerin sunayen ministcoin da ma'aikatunsu:
- Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin na Dijita - Bosun Tijani
- Ƙaramin Ministan Muhalli - Ishak Salaco
- Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki - Wale Edun
- Ministar Harkokin Teku da Tattalin Arziki - Bunmi Tunji
- Ministan Lantarki - Adedayo Adelabu
- Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Al'umma - Tunji Alausa
- Ministan Ma’adanai - Dele Alake
- Ministan Yawon Buɗe-Ido - Lola Ade-John
- Ministan Sufuri - Adegboyega Oyetola
- Ministan Kasuwanci da Zuba Jari - Doris Anite
- Ministan Wasanni - John Enoh
- Ministan Abuja - Nyesom Wike
- Ministar Al'adu - Hannatu Musawa
- Ministan Tsaro - Muhammad Badaru
- Ƙaramin Ministan Tsaro - Bello Matawalle
- Ƙaramin Ministan Ilimi - Yusuf T. Sununu
- Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane - Ahmed M. Dangiwa
- Ƙaramin Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane - Abdullah T. Gwarzo
- Ministan Kasafi da Tsare-Tsare - Atiku Bagudu
- Ministan Muhalli (Kaduna)
- Ƙaramar Ministar Abuja - Mairiga Mahmud
- Ministan Albarkatun Ruwa - Bello M. Goronyo
- Ministan Noma da Samar da Abinci - Abubakar Kyari
- Ministan Ilimi - Tahir Maman
- Ministan Harkokin Cikin Gida - Sa’Idu A. Alkali
- Ministan Harkokin Waje - Yusuf M. Tuggar
- Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a - Ali Pate
- Ministan Harkokin 'Yan Sanda - Ibrahim Geidam
- Ƙaramin Ministan Ƙarafa - U. Maigari Ahmadu
- Ministan Ƙarafa - Shuaibu A. Audu
- Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai - Muhammed IdrisMinistan
- hari'a - Lateef Fagbemi
- Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyuka - Simon B. Lalong
- Ƙaramar Ministar Harkokin Cikin Gida - Imaan Sulaiman-Ibrahim
- Ministan Ayyuka na Musamman - Zephaniah Jisalo
- Ministan Albarkatun Ruwa - Joseph Utsev
- Ƙaramin Ministan Noma da Samar da Abinci - Aliyu Sabi Abdullahi
Akwai ƙarin bayani...
Yanzu-Yanzu Tinubu ya naɗa Badaru da Matawalle ministocin tsaro, Wike ministan Abuja
August 16, 2023
0
Tags