Wannan ne karo na uku a cikin mako uku da manyan jami'an Amurka da Najeriya ke tattaunawa kan juyin mulkin ƙasar ta Nijar da ke Afirka ta Yamma.
Tinubu ne shugaban ƙungiyar Ecowas wadda ke jagorantar ƙoƙarin dawo da Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki, kuma ƙungiyar tana shirin tura dakaru don kawar da sojin da suka yi juyin mulkin.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Blinken ya ce ya kira Tinubu ''don jinjina wa ƙoƙarin Ecowas na dawo da turbar dimokuraɗiyya a Nijar''.
Ƴan Najeriya da dama ba su goyon bayan amfani da ƙarfin soji kan Nijar, har ma wasu sun gudanar da zanga-zangar ƙyamar matakin a birnin Kano da ke arewa maso yamma.