Sanarwar da Omar Aliu Toure, shugaban hukumar Ecowas, ya karanta bayan taron sirri da suka gudanar, shugabannin ƙungiyar sun ba da umarnin bijiro da dakarun ko-ta-kwana na Ecowas da yiwuwar tilasta wa Nijar aiki da ƙudurorin ƙungiyar ƙasashen.
Sun cimma wannan matsaya ce yayin taron gaggawa da suka gudanar ranar Alhamis a Abuja.
Cikin sauƙi, ba za a iya fayyacewa ƙarara, a kan ko umarnin yana nufin dakarun sojin Ecowas za su auka wa Nijar da yaƙi, ko kuma za su ɗaura ɗamara su zauna cikin shirin yaƙi ba ne kawai.
Tun da farko, Ecowas ta bai sojojin da suka yi juyin mulki wa'adin kwana bakwai don su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed da suka hamɓarar daga mulki, ko su fuskanci matakin amfani da ƙarfin soji.
Shugabannin sun ce sun yi nazari kan rahotannin jakadun da suka aika da kuma muhawara cikin tsanaki a kan shawarwarin da manyan hafsoshin tsaron Ecowas suka bayar da kuma sauran bayanan da hukumar ƙungiyar ƙasashen ta gabatar.
Sun kuma nanata Allah-wadai da juyin mulkin Nijar da kuma ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed.
Ƙungiyar ta ce za ta tabbatar da ganin ana aiki da duk ƙudurorinta kuma har yanzu duk ƙofofi a buɗe suke. Shugabannin sun kuma ɗora wa jagororin Ecowas alhakin ci gaba da bibiyar takunkuman da aka ƙaƙaba wa shugabannin juyin mulki a Nijar
Haka zalika, sun gargaɗi waɗanda suka ce suna kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Nijar su guji yin haka.
Da safiyar Alhamis ne shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma suka buɗe taron gaggawa na Abuja a ƙoƙarinsu na yanke shawarar ko su yi amfani da ƙarfin soja ko kuma hanyar diflomasiyya da nufin mayar da Nijar kan tsarin dimokraɗiyya, bayan juyin mulkin watan Yuli.
Mako biyu kenan da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka hamɓarar da Bazoum Mohamed daga kan mulki tare da tsare shi - a wani al'amarin juyin mulkin soji na baya-bayan nan da ke naso a faɗin nahiyar Afirka.
Shugabannin da suka isa Abuja don wannan taro sun haɗar da:
Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio
Shugaban Guinea Bissau, Umaro Mokhtar Sissoco
Shugaban Burundi Everiste Ndayishimiye
Shugaban Kwatdebuwa Alassane Ouattara
Shugaban Mauritania Mohamed Ould Ghazouani
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Senegal Macky Sall
Shugaban Benin Patrice Talon
Shugaban Najeriya kuma shugaban Ecowas Bola Tinubu.
Taron shi ne na biyu dangane da juyin mulkin Nijar a Abuja.
Haka zalika, taron na ranar Alhamis ya samu halartar wakilcin ƙasar Aljeriya, yayin da ministan harkokin wajen hamɓararriyar gwamnatin Bazoum, Hassoumi Massaoudou ya wakilci Nijar.
Sai kuma Mista Bankole Adeyoye daga Tarayyar Afirka da Mohammed Ibn Chambers, babban jami'in shirin Tarayyar Afirka mai taken "Kawo Ƙarshen Tashe-tashen Hankula".
Babu dai wani zaɓi mai sauƙi ga shugabannin na Ecowas, da Tinubu ke jagoranta.
Akwai matsin lamba a kansu na ganin sun mayar da tsarin dimokraɗiyya a Nijar - wata makekiyar ƙasa da ke fama da ɗumbin matsaloli kamar rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi da kuma talauci.
Sojojin da suka ƙwace mulki a Nijar ya zuwa yanzu sun yi ƙesasa ƙasa kan duk wani matsin lambar tattalin arziƙi da na diflomasiyya.
Ƙungiyar ta kuma yi barazanar amfani da ƙarfin soja. A 'yan shekarun baya, wannan na iya zama wani zaɓi da babu wata taƙaddama kansa.
Amma yanzu sauran ƙasashe masu maƙwabtaka da Nijar musamman Mali waɗanda a baya-bayan nan suka faɗa ƙarƙashin mulkin sojoji kuma suke samun tallafi daga sojojin hayar Rasha, suna goyon bayan janar-janar ɗin da suka yi juyin mulki a Nijar.
A jawabin buɗe taro da ya gabatar, shugaban ƙungiyar Ecowas, ya faɗa wa shugabannin da ke halarta cewa wa'adin kwaa bakwai da suka bai wa shugabannin juyin mulkin Nijar, kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.
Ya kuma shaida musu cewa ƙungiyar Ecowas ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya don cimma masalaha.
Ya ce ya yi farin cikin cewa ƙwararren jami'in diflomasiyya, Babagana Kingibe da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III da Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) sun halarci taron don bai wa shugabannin ƙasashen ƙungiyar ƙarin haske a kan ƙoƙarin shiga tsakani.
A cewarsa, jami'an sun halarci Libya da Aljeriya, inda suka samu tarba daga shugabannin ƙasashen masu maƙwabtaka da Nijar
Tinubu ya kuma bayyana cewa bisa matsayar da suka cimma a taronsu na farko, manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas sun yi taro daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Agusta, kuma za a gabatar musu da shawarwarin da suka bayar da ma wata muƙala da shugaban Hukumar Ecowas ya gabatar kan halin da ake ciki a Nijar.
Bayan jawabin ne kuma sai taron ya shiga zaman sirri, inda aka sallami 'yan jarida da sauran jami'ai.