Kano PILLARS ta bada Aron ɗan wasa zuwa kasar Serbia
Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sanar da bada Aron ɗan wasan gaban ta mai suna Abba Adam, wanda aka fi sani da Oscar zjwa ga FK Radnički Niš ta ƙasar Serbia.
Pillars ta wallafa a shafin ta na X cewa Oscar zai karasa kakar wasanni ta bana a can, inda ta kara da cewa a yarjejeniyar, akwai zabin sayen ɗan wasan da FK Radnički Niš za ta iya yi.
Oscar ya jefa ƙwallaye 5 a kakar wasa ta bana.
"Mun amince da aro dan wasan gabanmu Abba Adam Oscar ga kulob din FK Radnički Niš na Serbia a kakar wasa ta bana, tare da zabin siya.
"Oscar, wanda ya zura kwallaye biyar a gasar NPFL25, ba zai buga wasan da za Pillars za ta yi da Abia Warriors a yau ba.