Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, tare da hadin gwiwar Cibiyar Kwarewa ta Afirka kan Kiwon Lafiyar Jama’a da Tsare-Tsare (ACEPHAP) da ke Jami’ar Bayero, sun gudanar da taron gabatar da sakamakon bincike kokkafi kan mace-macen da ake samu a lokacin haihuwa (KASSEP).
Taron, wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, masana kimiyya, da shugabannin bangaren lafiya, ya gabatar da muhimman bayanai daga bangaren “Retrospect” na shirin, musamman sashen Verbal and Social Autopsy, wanda ya binciko dalilan mace-mace da kuma matsalolin zamantakewar da ke shafar lafiyar al’umma a jihar Kano.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Mai girma Dr. Abubakar Labaran Yusuf, wanda ya jagoranci taron tare da manyan jami’an Ma’aikatar, ya jinjinawa tawagar masu bincike bisa hazaka da jajircewarsu. Ya bayyana cewa ya shafe sama da shekara guda yana jiran cikakken rahoton.
“Wannan rahoto yana ba mu kwararan shawarwari da hanyoyi na rage mace-macen mata da kuma inganta lafiyar al’umma gabaɗaya a Jihar Kano,” in ji Dr. Yusuf. Ya kara da cewa zai mika rahoton ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, domin daukar matakan aiwatarwa ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Masana da suka taka muhimmiyar rawa a wajen taron, ciki har da Farfesa Ahmad Maifada Yakasai, Farfesa Baba Maiyaki Musa, da Farfesa Hadiza Shehu Galadanci, sun halarci taron tare da gabatar da muhimman bayanai daga binciken.
“Wannan hadin gwiwa ya nuna muhimmancin hada ilimi da aiki don cimma burin cigaban kiwon lafiya,” in ji Farfesa Galadanci.
“Jihar Kano na kara zama abar koyi wajen amfani da sahihan bayanai wajen yanke hukuncin lafiyar jama'a.”
Taron gabatar da rahoton ya tabbatar da kudurin gwamnatin jihar Kano na cigaba da inganta tsarin kiwon lafiya tare da kyautata ayyukan kula da lafiyar jama'a, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin gwamnati da cibiyoyin bincike.