Al’ummar Æ™aramar hukumar Gwarzo da ke Jihar Kano sun gudanar da sallar rokon ruwa domin neman saukar damina daga Allah Madaukakin Sarki.
Rahoton ya nuna cewa al’ummar garin sun fito a ranar Asabar inda aka gudanar da sallar tare da roÆ™on Allah da ya saukar da ruwa mai albarka.
Daga cikin addu’o’in da aka rika yi akwai roÆ™on kariya daga ambaliya, illa ga amfanin gona, da fatan samun noman damina cikin kwanciyar hankali.