Murabus: Na yabawa Ganduje da ya baiwa lafiyar da fifiko - Obi
ÆŠan takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar Labour a zaÉ“en 2023, Peter Obi, ya yaba wa Dr Abdullahi Ganduje bisa murabus da ya yi daga matsayin Shugaban jam’iyyar APC na Æ™asa.
A jiya Juma'a ne dai Ganduje ya mika takardar murabus dinsa ga Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na jam’iyyar (NWC) ta hannun Sakatare na Ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya ambaci dalilan lafiya a matsayin abin da ya sa ya yanke shawarar sauka daga mukamin.
Sai dai kuma Obi, tsohon gwamnan Anambra, ya bayyana jinjinarsa a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Juma’a.
A cewarsa, ya karanta rahoton labarai cewa Ganduje ya yi murabus daga mukaminsa nan take, yana ambaton matsalolin lafiya a matsayin dalili.
“Ina son in yaba wa Ganduje bisa fifita lafiyarsa fiye da komai.”
Obi ya kuma yi kira ga sauran masu riƙe da mukamai da su yi koyi da Ganduje.