Jigo a Siyasar Jihar Kano ya rasu sanadiyyar hatsarin mota
Allah ya yi wa babban Dan Siyasa kuma tsohon Shugaban Karamar Hukumar Dala Alhaji Mahmud Sani Madakin Gini rasuwa.
Marigayin ya zama Shugaban Karamar hukumar Dala a zamanin mulkin Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekaru.
Bayan kammala wa'adin mulkin sa, marigayin ya yi shura wajen gwagwarmaya a siyasance,
Mahmud Sani Madakin Gini, wanda ake wa laƙabi da Buharin Dala, ya rasu a safiyar Litinin din nan sakamakon hatsarin mota a hanyarsa ta dawo wa daga Abuja.
Za a gudanar da jana’izarsa da karfe 5:00 na yammacin yau a gidansa da ke unguwar Yalwa a Dala.