An kira ga kotun koli ta gaggauta yanke hukunci akan shari’ar masarautar Kano
Gamayyar Ƙungiyar masana harkokin siyasa masu kare dimokuraɗiyya da shugabanci na gari, ta roƙi kotun koli ta gaggauta yanke hukunci akan shari’ar masarautar Kano.
Kungiyar tace tabbas al’umma na bukatar babbar kotun ta kammala wannan shari’a ta masarautar Kano, wadda aka shafe lokaci mai tsawo ana yin ta.
Bukatar hakan na cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis 10 ga watan Yuli, ɗauke da sanya hannun shugabanta na ƙasa Kwamared Al-Amin Albarra, da sakataren sa Malam Saminu Abubakar.
A cewar Kungiyar ta damu matuƙa dangane da yadda rikicin masarautar Kano ke neman rikiɗewa zuwa tashin hankali da janyo sauran matsalolin da ba zasu haifar da ɗa mai ido ba, in har ba’a kammala shari’ar masarautar ba.