JAMB ta aiyana maki 150 a matsayin mafi karanci na shiga jami'a a Nijeriya
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i ta Ƙasa (JAMB) ta sanya makin 150 a matsayin mafi Æ™anÆ™anta ga É—alibai don shiga jami’o’i a Æ™asar nan.
JAMB ta yanke wannan shawara ne a ranar Talata yayin Taron Tsare-tsaren Shiga Makarantu na 2025 da aka gudanar cibiyar taro ta kasa da ke Abuja.
Hukumar ta bayyana cewa mafi karancin maki ga kwalejojin koyar da aikin jinya shi ne 140, kwalejojin noma 100, sannan kuma kwalejojin ilimi 100.
“An kayyade mafi Æ™arancin makin da za a yarda da shi wajen karÉ“ar É—alibai a zangon karatu na gaba da 150 ga jami’o’i, 100 ga kwalejojin fasaha (polytechnics), 100 ga kwalejojin ilimi, da kuma 140 ga kwalejojin koyar da aikin jinya, bisa amincewar shugabannin manyan makarantu,” in ji JAMB a shafinta na X.