Shekarau da shugabannin PDP sun ƙaurace wa Atiku a yayin da ya kawo ziyarar ta'aziyyar Dantata a Kano
Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, tare da daukacin shugabannin jam’iyyar PDP a jihar, sun yi watsi da ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata a ranar Lahadi.
Shekarau, wanda mamba ne na kwamitin amintattu na PDP kuma jagoran adawa a Kano, ba a ga fuskar sa ba a cikin tawagar manyan jami’an da suka raka Atiku yayin ziyarar ta’aziyyar da suka kai gidan marigayi Dantata dake Koki.
Ko da yake tsohon dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023 bai fice daga jam’iyyar a hukumance ba, Amma alakar dake bayyana tsakaninsa da jam'iyyar hadaka ta ADC na iya zama dalilin wannan martani daga shugabannin PDP.
Sai dai Atiku ya samu rakiyar tsohon Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami; tsohon gwamnan Jihar Adamawa, Umaru Jibrilla Bindo; da wasu fitattun manyan jami’ai.
Da aka tuntubi shugaban PDP na Kano, Alhaji Yusuf Ado Kibiya, ya shaida wa wakilinmu cewa jam’iyyar adawa a jihar bata da masaniyar ziyarar Atiku.
Ko da yake shugaban ya ce bai da tabbacin ko tsohon mataimakin shugaban kasa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP ba, amma ya jaddada cewa babu dalilin da zai sa shugabannin PDP su raka Atiku zuwa gidan Dantata.