Ƴan sanda a jigawa sun kama magidancin da ya kashe tsohowar matarsa
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama wani magidanci mai suna Iliyasu Musa ɗan shekaru 40 daga ƙauyen Dangewaye da ke Aujara, bisa zargin kashe tsohuwar matarsa, Hadiza Sale, mai shekaru 30, wadda suka haifi ’ya’ya shida tare.
Wannan na cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Shi’isu Lawan Adam, ya fitar a ranar Alhamis 24 ga Yuli, 2025.
Sanarwar ta ce tun ranar 10 ga Yuli 2025 ne wanda ake zargin ya makawa tsohuwar matar tasa sanda a ka yayin da ta ke dawowa daga kasuwa a Afasha, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarta sannan ya tsere.
Bayan kwana 13 da faruwar lamarin, ’yan sanda daga Aujara suka kama Iliyasu a ƙauyen Larabar-Tambarin-Gwani inda ya buya.
Yanzu haka yana sashen binciken manyan laifuka na shalkwarar yan sanda da ke Dutse, inda ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da shi a kotu.