Mutane 2 sun Mutu sakamakon fadawa Rijiya a Karamar hukumar Kura dake Kano
Al’ummar unguwar Lungun Wali da ke Æ™aramar hukumar Kura a Jihar Kano sun shiga firgici, bayan da mutum uku suka faÉ—a cikin wata tsohuwar rijiya a yankin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar biyu daga cikinsu.
Wani mazaunin yankin, Yusuf Sulaiman Kura, ya shaida wa jaridar Neptune Prime cewa sun shiga zullumi sakamakon alʼamarin.
Rahotonni sun ce wani yaro ne ya fara faÉ—awa cikin rijiyar, sai wani ya shiga domin cetonsa amma shi ma ya makale, sannan na uku ya bi su ciki, amma shi ma bai iya fita ba.
Daga bisani jami’an kwana-kwana suka isa wajen, suka ciro su uku daga rijiyar, amma mutum É—aya ne kawai a raye, wanda aka garzaya da shi asibiti domin samun taimakon gaggawa.