Tunda fari dai Yan Sanda ne su ka gurfanar da matasan a gaban kotun karkashin jagorancin mai sharia Nura Yusuf Ahmad dauke da takardar tuhume tuhumen hadin baki domin aikata laifi da tada hankalin jama’a.
Matasan dai wato Ali Nasir da Bashir Garba da Jabir Abdulmumini da kuma Abubakar Saidu dukkan su mazauna garin Yamadi da ke Karamar Hukumar Gezawa kuma bayan karanto musu nan take su ka amsa laifinsu kotun kuma ta aike da su gidan gyaran hali har zuwa ranar Alhamis kuma da ma tun ranar 9-07-2025 aka aike dasu.
An dai same su da Daura Auren Ali Nasir da wata budurwa wato Fiddausi Arma.
Lamarin kuma ya faru dai dai lokacin da Fiddausi ta zo wucewa ta inda su ke hira sai Ali ya ce da abokansa yana so a Daura masa aure da ita nan take ya zaro kudi Naira dubu biyu da dari Tara da hamsin ya kuma kawo alewa.
Shi kuma Buhari Garba ya fito a matsayin liman, jabir ya zama waliyinta Abubakar kuma waliyinsa.
Nan take aka daura aure mahaifinta yana Gona aka buga masa waya ake tayashi murna abin da ya ba shi mamaki bayan ya dawo gida ya sami wannan aika aikar, daga bisani yai kara wajan Yan Sanda hakan ya sa aka gurfanar da su a gaban kotun.