Kamfanin Man fetur na Dangote ya sanar da karin rangwamen farashin man fetur, inda sabon farashin ya koma Naira 820 a kowace lita daga Naira 840 da aka sayar a baya.
A cewar kamfanin, sabon farashin ya fara aiki daga jiya Talata, 8 ga Yuli, 2025.
Wannan sauyi na nufin ragin Naira 20 ne daga tsohon farashin man da kamfanin ke saidawa.
Sabon matakin na zuwa ne kasa da mako guda bayan Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) ya rage farashin sayar da Mai daga Naira 945 zuwa Naira 910 a kowace lita.
Rangwamen na Dangote ya biyo bayan wani sauyin farashin da kamfanin ya yi makon da ya gabata, inda ya saukar da farashin daga Naira 880 zuwa Naira 840.