Maƙabartu da dama na cikin wani hali a Kano – Ƙungiyar masu haƙan Kabari
Ƙungiyar masu haƙan Kabari ta jihar Kano, ta bayyana damuwar ta kan yadda ake samun ƙarancin kulawa a mafi yawan maƙabartu a sassan jihar nan, la’akari da yadda hakan ke haifar da ruftawar ƙabarurruka musamman ma a wannan lokaci na Damuna.
Shugaban ƙungiyar a jihar Kano, kuma guda cikin masu haƙan Ƙabari a maƙabartar Abbatuwa, Muhammad Inuwa Umar, shi ne ya bayyana hakan a zantawar sa da waliyar Neptune prime a jiya Talata 08 ga watan Yulin 2025.
Ya kuma ce mafi yawan maƙabartu na neman tallafin Ƙasa, da Tukwane, da Tebur, da Baro da kuma Adda, da dai sauran su, domin samun dama wajen kaucewa ruftawar ƙabarurruka a maƙabartun.
Muhammad Inuwa, ya kuma ce akwai buƙatar suma masu haƙan Ƙabari a maƙabartu a ƙara himma wajen kula da wal-walar su, domin suma suna cikin halin damuwa bisa yadda alawus ɗin da ake basu yake gaza magance musu ɗawainiyar yau da gobe.
“Yanzu haka Maƙabartu da dama na cikin wani hali bisa yadda mafi yawancin ƙabarinsu a Kano ke ruftawa musamman ma a wannan lokaci na Damina da ake ciki, don haka ya kamata a kawo ɗauki, in ji shi”.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu daga cikin maƙabartu suka fara fuskantar ruftawa a wannan lokaci na Damuna, al’amarin da jama’a ke ci gaba da neman a kai musu ɗauki don daƙile matsalar.