Jami'ar Bayero ta Kano, ta zabi Farfesa Haruna Musa a matsayin sabon shugaban jami'ar.
Musa ya zama shugaban ne bayan jami'ar ta gudanar da zaɓe tsakanin ƴan takarar kujerar a yau Talata a harabar jami'ar.
Ga jerin yadda sakamakon zaɓen ya kasance:
1. Farfesa Haruna Musa = 853
2. Farfesa Mahmoud Umar Sani = 367
3. Farfesa Muhammad Sani Gumel = 364
4. Farfesa Adamu Idris Tanko = 161
5. Farfesa Bashir Muhammad Fagge = 18