Wata Kotu a Kano ta yankewa wa wani matashi da ya cinnawa budurwarsa wuta Daurin Shekaru 15
Babbar kotun jihar Kano mai lamba 1 Æ™arÆ™ashin jagorancin Mai shari’a Dije Abdu Aboki ta yanke wa wani matashi daga Æ™aramar hukumar Takai hukuncin daurin shekaru 15 a gidan gyaran hali, bisa laifin yunkurin kisan kai ta hanyar cinnawa budurwarsa wuta.
An gurfanar da matashin mai suna Abdullahi Saidu, É—an asalin garin Sakwaya da ke Æ™aramar hukumar Takai, bisa zargin cinnawa budurwarsa Sa’adatu Ibrahim wuta saboda an dawo masa da kayan auren da ya kamata.
Kotun ta saurari shaidu uku daga masu gabatar da ƙara kuma lauyoyin gwamnati Barista Hajara Ado Sale da Barista Sadiya Sambo da kuma shaida ɗaya daga ɓangaren wanda ake ƙara.
Bayan nazarin shari’ar, kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 15, tare da umarnin ya biya diyyar Naira miliyan É—aya ga wadda abin ya shafa, ko kuma Æ™ara shafe shekaru 5 a gidan yari idan ya kasa biyan kudin.
Bayan zaman kotu, Barista Hajara Ado Sale ta ce hukuncin ya dace da nauyin laifin, yayin da lauyoyin wanda aka yanke wa hukunci suka ƙi cewa komai ga manema labarai.