Civil Defence a Kano ta kama mutane 9 da ake zargi da satar murafan magudanen ruwa na karfe da Solar Panels
Hukumar Tsaron Civil Defence a Jihar Kano ta kama mutane 9 da ake zargi da satar kayayyakin gwamnati a sassa daban-daban na jihar, ciki har da murafan magudanan ruwa na ƙarfe da Solar Panel.
Kakakin hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Hukumar ta ce, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, an kama mutum bakwai da ake zargi da satar murafa goma na ƙarfe daga magudanar ruwa.
Jami’an tsaro da ke bakin aiki ne suka damke su, kafin daga baya bincike ya kai ga kama karin mutum biyu da ake zargi da sayen kayan sata.
Wadanda aka kama sun haÉ—a da Abubakar Umar, Sadiq Jafar, Iliya Nasir, Abba Muhammad, Al-ameen Idris, Shamsu Ibrahim Usman, da Yusuf Abdulmumini.
An kwato murafa goma da mota kirar Mercedes Benz daga hannunsu.
A wani lamari daban, an kama Haruna Musa da Sadiq Suleiman da ake zargi da satar Solar Panel guda huÉ—u a kasuwar Kanawa Economic City dake a Kano.
Kakakin hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya ce za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.