Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin lafiya, kuma rahotanni sun ce kwanan nan aka sallame shi daga dakin kula da masu matsananciyar rashin lafiya (ICU) a wani asibiti da ke Landan a kasar Birtaniya.
Wani makusancin tsohon shugaban ya bayyana cewa Buhari ya kamu da rashin lafiya ne a Landan yayin da ya je don duba lafiyarsa.
Rahoton ya ce an kwantar da Buhari a dakin ICU, amma daga bisani aka sallame shi makon da ya gabata.
Ko da ya ke ba a bayyana irin cutar da ke damunsa ba, rahotanni sun nuna cewa yana samun sauki a Landan, kuma ana sa ran zai dawo Najeriya da zarar ya warke gaba É—aya.
Bisa bayanan daga wasu majiyoyi masu tushe, Mamman Daura – kawun Buhari kuma amintaccensa – shima yana samun sauki daga rashin lafiya a kasar Birtaniya.
Buhari bai halarci bikin cika shekaru 50 da kafuwar Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) da aka gudanar a Legas ranar 28 ga Mayu ba.
A wata wasika da ya aika wa Shugaba Bola Tinubu, Buhari ya bayyana cewa rashin halartar sa taron ya samo asali ne daga tafiyarsa ta duba lafiya a Birtaniya.