Za ai Jana'izar Aminu Dantata a Madina bayan sallah La'asar
An tabbatar da cewa za a gudanar da jana’izar fitaccen attajiri Alhaji Aminu ÆŠantata a masallacin Madina bayan sallar La’asar a ranar Talata.
Mustapha Junaid, wanda shi ne mataimaki na musamman ga marigayin, ya tabbatar wa BBC cewa dukkan shirye-shirye sun kammala.
“Alhamdu lillah, an É—auki marigayin daga filin jirgin sama na Madina, yanzu haka za a kai shi Shakzura domin Æ™arin shirya gawar, kafin daga bisani a tafi da shi haramin Madina don gudanar da sallah, kamar yadda hukumomin Saudiyya suka amince,” in ji Mustapha Junaid.
Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu ne a ranar Asabar yana da shekara 94 a ƙirgar miladiyya, sai kuma shekara 97 a ƙirgar Hijira, kamar yadda sakatarensa Mustapha Abdullahi ya bayyana wa BBC.